🌐 SHIN KA TAƁA TAMBAYAR TA YAYA KAMFANONIN SADARWA KAMAR (MTN, AIRTEL DA SAURANSU) KE SAMAR DA DATA?


Yawancinmu muna amfani da data kowace rana, amma ka taɓa tambayar kanka “Daga ina suke samo ta?”

To bari ku ji

📡 1. Suna Sayo Karfin Sadarwa ( Wato Bandwidth) daga Manyan Masu Samarwa Da’ita


Suna siyo babban bandwidth daga manyan Internet Providers na ƙasa da ƙasa (misali: Google / Alphabet (Equiano Cable, Dunant Cable),


Meta / Facebook (2Africa Cable),

$ads={1}

MTN GlobalConnect (Africa to Europe fiber routes),


Orange Marine (West Africa Cable System - WACS) DSS.


Kamfanonin sadarwa kamar (MTN) na shigar da wannan ƙarfin sadarwar (Bandwidth) cikin ƙasa ta manyan hanyoyin fiber optic cables da kuma satellite links.


🏙 2. Suna Shigar da Bandwidth Cikin Birane da Kauyuka


Ana rarraba bandwidth ɗin zuwa Service Nodes ko Base Stations (BTS towers) wato ƙarfen service.


A wasu wurare, zaka ga wata waya mai tsawo a cikin pipe ana sakata cikin ƙasa — wannan ita ce fiber optic, mai ɗaukar siginar internet cikin sauri.



📲 3. Suna Raba ta ga Masu Amfani


Sigina daga tower (ƙrfen service) yana shiga waya ta hanyar 3G, 4G ko 5G bands.


Kamfanonin suna tsara packages kamar 1GB, 10GB, ko unlimited, sannan su sayar.


Bandwidth ɗin da suke siya, suna raba shi zuwa dubban mutane (shared capacity).


💰 4. Ta Yaya Suke Cin Riba?


Suna siya bandwidth mai yawa da farashi mai rahusa daga manyan masu samarwa (Internet Providers).


Sannan su raba shi cikin data bundles da farashi maii tsada.


Misali: 1GB da suka siya yana iya kai musu ₦100, amma su sayar ₦350.


Sannan suna saka speed limit ko fair usage policy don kada ka cinye bandwidth ɗin da yawa.


⚙ Me Amfanin Wadannan “Pipes da Antennas” da kake gani a gari?


Pipes da fiber cables: Suna kawo babban signal daga cibiyar sadarwa zuwa tower ( karfen service).


Antennas: Suna aika siginar zuwa wayoyinmu ta hanyar rediyo waves.


To wanna shine Allah ya sa mu dace amen summa amen

Post a Comment

DISCLAIMER:
Comments published here does not reflect the sole opinion of our affiliates or any employee thereof. *

Previous Post Next Post

Advertisment

Advertisment