Manchester City za ta iya sayen dan wasan Argentina Lionel Messi, mai shekara 33, idan kwangilar shi ta kawo karshe a Barcelona a badi idan kuma Pep Guardiola ya bar kulub din.
(Talksport)
Chelsea na diba yiyuwar sayar da 'yan wasanta shida domin samun kudin da za ta karbo dan wasan Jamus Kai Havertz, mai shekara 21, wanda darajarsa ta kai fam miliyan £90m a kungiyarsa ta Bayer Leverkusen. (Express)
Arsenal da Napoli na hamayya kan dan wasan gaba na Newcastle da Faransa Allan Saint-Maximin, mai shekara 23. (Le10 Sport in French)
Arsenal za ta fara tattaunawa kan makomar dan wasan Faransa Alexandre Lacazette, mai shekara 29. (Mirror)
Paris St-Germain na tunanin dauko dan wasan
Arsenal da Spain Hector Bellerin, mai shekara 25, yayin da kuma Juventus da Bayern Munich ke son dan wasan. (Express)
$ads={1}
Dan wasan tsakiya naBayern Munich Thiago Alcantara, mai shekara 29, na matukar son komawa taka leda a gasar Premier a Liverpool
da ke son sayen dan wasan na Sifaniya kan fam miliyan 32. (Mail)
Sai dai kocin Bayern Hansi Flick na kokarin shawo kan Alcantara ya ci gaba da zama a kulub din. (Sun)
Dan wasa baya na Ingila Danny Rose, mai shekara 30 yana ganin rayuwarsa a Tottenham ta kawo karshe inda yake ci gaba da nuna kwazo a
Newcastle da ta karbi aronsa . (Mirror)
Sevilla da Atletico Madrid na nazari kan dan wasan Barcelona da Croatia Ivan Rakitic, mai shekara 32, wanda ke dab da barin Nou Camp a wannan bazara. (Marca)
Barcelona ta gamu da cikas a kokarinta na daukar Xavi a matsayin sabon kocinta bayan tsohon dan wasan nata na tsakiya ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya da kungiyar Qatar ta Al-Sadd . (Mail)
Kocin Everton Carlo Ancelotti ya ce ba zai sayar da manyan 'yan wasansa ba inda dan wasan Faransa Lucas Digne, mai shekara 26, da dan wasan gaba na Brazil Richarlison, mai shekara 23, da kuma dan wasan baya na Ingila Mason Holgate, mai shekara 23, ake tunanin suna dab da ficewa Goodison Park. (Talksport)
Manchester United ta yi nadamar rashin dauko dan wasan gaba na Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 19, kafin ya koma Borussia Dortmund daga Red Bull Salzburg a cewar tsohon dan wasan kulub din Paul Scholes. (Mail)
Dan wasan gaba na Croatia Mario Mandzukic, mai shekara 34, yanzu ya kasance ba shi da kungiya bayan ya kawo karshen yarjejeniyarsa da kungiyar Qatar ta Al-Duhail . (Goal)